Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

An Sake Sako Ɗalibai 10 Na Sakandaren Bethel Baptist Ta Kaduna

  Daga Muhammad Farouk Ƴan bindiga sun sako ɗalibai 10 da aka sace watanni biyu da suka gabata daga makarantar Sakandare ta Bethel Baptist a...

 

Daga Muhammad Farouk

Ƴan bindiga sun sako ɗalibai 10 da aka sace watanni biyu da suka gabata daga makarantar Sakandare ta Bethel Baptist a jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce an saki ɗaliban ne a ranar Asabar bayan shafe sama da wata biyu a hannun ƴan bindiga. Rukuni na uku ke nan na ɗaliban da ƴan bindigar suka sako inda dhugaban Baptist, Rabaran Joseph Hayab, ya ce har yanzu akwai ɗalibai 21 a hannun ƴan bindigar.

Ya kuma kara da cewa ƴan bindigar sun bukaci a biya kudin fansa da ba a bayyana kan ko wane ɗalibi, inda ya bayyana abin da ƴan fashin ke yi a matsayin azabtar da iyayen da ba a sako ƴaƴansu ba.

Wannan ne karo na 10 da aka yi garkuwa da mutane a jihar Kaduna tun watan Disamba.


No comments