Daga Ammar Muhammad Bayan shafe kwanaki 13 a hannun ‘yan bindiga, daliban da aka yi garkuwa da su na makarantar Sakandaren Gwamnati dake...
Daga Ammar Muhammad
Bayan shafe kwanaki 13 a hannun ‘yan
bindiga, daliban da aka yi garkuwa da su na makarantar Sakandaren Gwamnati dake
Kaya a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara sun shaki iskar ‘yanci.
Gidan Talabijin na kasa, NTA ne ya
wallafa labarin a sahihin shafinsa na Facebook a ranar Litinin.
NTA ta labarta cewa dalibai guda 75
sun samu ‘yancinsu, amma ba su yi karin bayani kan yadda aka ‘yanto daliban ba.
Labarin na NTA ya wallafa cewa ne; “Dalibai
75 na makarantar Sakandaren Gwamnati dake Kaya a karamar Hukumar Maradun ta
jihar Zamfara, wadanda aka yi garkuwa da su mako biyu da ya gabata, sun shaki
iskar ‘yanci”.
A ranar 1 ga watan Satumban 2021 ne,
‘yan sandan jihar Zamfara, suka bayyana labarin sace daliban bayan da ‘yan bindiga
suka kai wa makarantar hari.
No comments