Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Toshe Layukan Sadarwa A Sokoto

  An toshe layukan sadarwa a jihar Sokoto fiye da mako biyu bayan an toshe hanyoyin sadarwar a jihar Zamfara da ke makwaftaka da Jihar. Gwam...

 


An toshe layukan sadarwa a jihar Sokoto fiye da mako biyu bayan an toshe hanyoyin sadarwar a jihar Zamfara da ke makwaftaka da Jihar.

Gwamnatin jihar ta tabbatarwa BBC ta matakin, inda kakakin gwamnan jihar Muhammad Bello ya ce an toshe layukan ne a ƙananan hukumomi 14 na jihar.

Wasu mutanen jihar sun ce idan an kira layukan MTN ba a kamawa, wasu kuma sun ce matsalar ta shafi har da masu amfani da layin Airtel.

Matakin toshe layukan na sadarwa ya shafi yankunan jihar Katsina da ke makwabtaka da jihar Zamfara.

Hukumomin jihohin sun ce an ɗauki matakin domin ƙoƙarin magance matsalolin ƴan bindiga masu kai hare-hare da satar mutane a jihar.

Toshe layukan na zuwa bayan wasu Æ´an bindiga sun abka garin Tangaza sun kashe mutane tare da satar abinci.

No comments