Rahoton BBC Hausa An toshe layukan sadarwa a wasu sassa na jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, kusan mako guda kenan bayan an toshe na ...
An toshe layukan sadarwa a wasu sassa na jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, kusan mako guda kenan bayan an toshe na jihar Zamfara da ke makwaftaka da Jihar.
Mai bai wa gwamnan Katsina shawara a kan harkokin tsaro Ibrahim Ahmed Katsina ne ya tabbatar wa BBC da batun katse layukan inda ya ce an É—auki matakin ne domin inganta tsaro a jihar.
Ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa sun haɗa da Funtua da Bakori da Jibiya da Malumfashi da Faskari da Batsari da Ɗanmusa.
Sauran kuwa su ne Sabuwa da Kankara da Dutsinma da Kurfi da Safana da ÆŠandume.
A cewar Ibrahim Kastina, ya zama wajibi gwamnatin Katsina ta É—auki wannan mataki, domin hana Æ´an bindigar da ke Zamfara gangarawa Katsina su ci gaba da amfani da waya da gudanar da harkokinsu.
Akasarin ƙananan hukumomin da aka toshe hanyoyin sadarwar na makwabtaka da Zamfara da kuma Kaduna sakamakon yadda yanayin tsaro ya ƙara ƙamari a jihohin, in ji Ibrahim Katsina.
"Maƙasudin wannan mataki shi ne hana yaɗuwar ta'addanci, duk inda muka ga yana yaɗuwa to za mu toshe amma a halin yanzu waɗannan ƙananan hukumomin da abin ya yi ƙamari aka toshe domin a samu cin ƙarfin abin kuma a taimaka wa jami'an tsaro su samu gudanar da aikinsu cikin sauƙi", a cewarsa.
Ya kuma bai wa jama'ar ƙananan hukumomin da abin ya shafa haƙuri inda ya ce an ɗauki wannan matakin ne domin jama'a su samu sauƙin wannan lamari.
A makon nan ne dai aka yi ta yaÉ—a wata takarda a shafukan sada zumunta inda takardar ke cewa hukumar kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya wato NCC ta bayar da umarni a rufe hanyoyin sadarwa a Katsina.
Sai dai gwamnatin Katsinar ta bakin mai magana da yawun gwamnan jihar Abdu Labaran ya fito ya ƙaryata batun inda ya ce shugaban NCC ya tabbatar wa gwamnatin Katsina da cewa takardar ta bogi ce.
A makwabciyar Katsina wato Zamfara ne aka fara ɗaukar wannan mataki, tare da hana sayar da fetur a jarka da rufe wasu kasuwanni na mako-mako, matakin da ita ma jihar Katsina da wasu makwaftansu suka dauƙa.
Jihohin Katsina da Zamfara da Kaduna da Neja na cikin jihohin da Æ´an bindigan ke cin karensu babu babbaka. Haka ma sauran jihohin da ke makwabtaka da waÉ—annan ana samun hare-haren jefi-jefi kamar Sokoto da Nasarawa.
Sai dai rahotannin da ake samu na baya-bayan nan na cewa jam'ian tsaro sun fara samun nasara a kan ƴan bindigar da ke dazukan Zamfara inda aka yi musu ɓarin wuta ta sama da ƙasa, da ƙwace makamansu da kashe da dama daga cikinsu.
No comments