Gwamnatin jihar Kaduna ta Nasiru Ahmad El-Rufai ta sanar da kisan Rabaran Silas Yakubu Ali, wani Fasto a cocin ECWA da ke Kibori-Asha ...
Gwamnatin jihar Kaduna ta Nasiru Ahmad El-Rufai ta sanar da kisan
Rabaran Silas Yakubu Ali, wani Fasto a cocin ECWA da ke Kibori-Asha Awuce a
karamar hukumar Zangon Kataf.
Samuel Aruwan, Kwamishinan tsaro na jihar ya ce an samu gawar Faston
ne da safiyar jiya Lahadi a Kibori. Sanarwar ta bayyana cewa Rabaran Silas Yakubu Ali ya tafi Kafanchan ne
ranar Asabar, daga nan ba a sake jin duriyarsu ba.
Ya ce yanzu haka jami'an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike don
gano masu hannu a kisan.
No comments