Rahotanni daga jihar Katsina na cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da kanwar mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Shehu Dalhatu T...
Rahotanni daga jihar Katsina na cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da kanwar mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Shehu Dalhatu Tafoki kamar yadda BBC Hausa suka labarto.
An sace Asama'u Dalhatu ana tsaka da shirye-shiryen soma bikinta, a cewar É—an majalisar.
Ƴan bindigar sun kai hari ne kauyen Tafoki da ke karamar hukumar Faskarin Katsina tare da sace Amaryar.
A lokacin tabbatar da faruwar lamarin, É—an majalisar ya shaida wa jaridar Daily Trust cew an sace kanwar tasa da sanyin safiyar Lahadin.
Ya kara da cewa har yanzu 'yan bindigar ba su tuntube su ba domin neman kudin fansa.
No comments