Ministan kula da Harkokin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio ya ce rahoton binciken da aka yi kan Hukumar Ci gaban yankin na Neja Delta N...
Ministan
kula da Harkokin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio ya ce rahoton binciken da
aka yi kan Hukumar Ci gaban yankin na Neja Delta NDDC, ya nuna cewa akwai
ayyuka sama da dubu 13 da aka yi watsi da su a yankin.
Sanata
Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar
Alhamis a Abuja, lokacin da ya mika rahoton binciken ga shugaban kasa Muhammadu
Buhari ta hannun ministan shari’a, Abubakar Malami.
Akpabio
ya ce tun kafin gabatar da rahoton wasu ‘yan kwangila suka koma kan aikin su da
kan su, kuma kawo yanzu sun kammala ayyukan hanyoyi kusan 77.
Yankin
na Neja Delta na ci gaba da zama koma baya tun daga shekarar 1958, duk da
kokarin gwamnatocin baya ta hanyar kirkirar shirye -shirye da ayyuka
daban-daban domin bunkasa yankin.
A
halin da ake ciki dai, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa
gwamnatinsa za ta tabbatar ta kwato sama da Naira tiriliyan 6 da ake zargin an
karkatar da su a yayin gudanar da ayyukan hukumar NDDC tsakanin shekarar 2001
zuwa 2019.
No comments