Hoton wani dalibi dan Nijeriya a kan Keke a daidai lokacin da ake ruwan sama ya ja hankalin ma’abota shafukan sada zumunta musamman a Face...
Hoton wani dalibi dan Nijeriya a kan Keke a daidai lokacin da ake ruwan sama ya ja hankalin ma’abota shafukan sada zumunta musamman a Facebook, inda aka baza cigiyar nemansa domin gano inda yake don a ba shi tallafi na musamman.
Dalibin wanda hoton ya nuna shi sanye da kayan makaranta farare a kan Keke yana zuba gudu akan Kekensa domin isa makaranta, ya ja hankalin wani dan Nijeriya ma’abocin shafukan sada zumunta mai suna Ibrahim Sanyi-Sanyi, inda ya baza hoton na shi yana neman inda za a gan shi.
![]() |
Hoton Dalibin |
Ibrahim Sanyi-Sanyi ya wallafa hoton
dalibin a turakarsa ta Facebook, inda ya nemi jama’a da su taimaka masa wajen
gano inda dalibin yake, inda ya ce suna son bai wa wannan dalibi mai kwazo
gudummawa ne.
Mutane da dama suma sun alkawuranta
cewa za su tallafa wa dalibin in dai har an gano shi wajen ganin dalibin ya
cimma gaci.
Ya zuwa hada rahoton nan, cigiyar
dalibin, mutum 630 ne suka raba shi ga sauran abokansu a Facebook din.
No comments