Daga
Wakilinmu
Sama da Naira Miliyan 345 ne aka
nema aka rasa a Asusun Kotun Shari’a ta Kano kamar yadda gidan Rediyon Freedom
suka labarto.
Babban Alkalin jihar, Tijjani
Yakasai ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka kai rahoton lamarin
gaban Hukumar karbar korafe-korafen al’umma da yaki da cin hanci ta jihar Kano,
PCACC domin gudanar da bincike.
Sakataren kotun, Haruna Khalil, ya
ce an kafa kwamitin bincike kan batun.
A cewarsa kudin ma marayu ne da aka
ajiye a kotun kafin a kai ga bayar da shi ga masu hakki.
A cewarsa murfin ya bude ne a daidai
lokacin da kotu ta yi kokarin cire wani bangare na kudin, sannan ta gano cewa
Naira miliyan 9 kacal ya rage a cikin asusun.
Bayanai sun nuna cewa bayan kafa
kwamitin bincike, an sake wadansu na’urorin kwamfuta a Hukumar domin rufe
abubuwan da suka wakana.
Mukaddashin
Hukumar karbar korafe-korafen al’umma da yaki da rashawa ta Kano, Mahmud
Balarabe, ya ce sun gayyaci kafatanin wadanda suke da hannu a ciki tare da jami’an
Bankin domin yi musu tambayoyi.
0 Comments