Rahotanni na cewa ana zargin wata mata da hallaka 'ya'yan kishiyarta uku ta hanyar saka masu guba a cikin shayi. Lamarin ya fa...
Rahotanni na cewa ana zargin wata
mata da hallaka 'ya'yan kishiyarta uku ta hanyar saka masu guba a cikin shayi.
Lamarin ya faru ne a garin Patiskum
na jihar Yobe da ke yankin arewa masu gabashin Nijeriya.
BBC ta labarto cewa a yanzu haka
matar na hannun ‘yan sanda kuma tuni suka soma bincike kan lamarin.
Akwai kuma ɗa namiji daya da mace
biyu kwance a Aassibiti suna jinya.
Maigidan matar Alhaji Haruna ya
tabbatar da faruwa al'amarin a wani tattaunawa da BBC, sannan ya ce yanzu haka
sun sanar da mahukunta domin daukan mataki.
Kakakin ‘yan sandar Yobe ASP Dungus
Abdulkarim ya tabbatar da mutuwar yaran, kuma ya shaida cewa yanzu haka suna
kan bincike.
No comments