Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta ce za ta iya bai wa tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan damar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 idan ya shigar jam'iyyar. Ya ce komawar jonathan APC zai zama babban abun alfahari a gare su.
Jaridar The Cable ta rawaito cewa John Akpanudoedehe, sakataren kwamitin riko na jam’iyyar APCn na bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Channels.
Ya ce za a ba Jonathan damar yin takarar kujerar shugaban kasa a 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar, kamar kowane mutum mai sha’awar tsayawa takara.
“Za mu yi masa maraba; hakan kuma zai karfafa jam’iyyar, ”in ji Akpanudoedehe.
0 Comments