Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Babu Ranar Bude Layukan Sadarwa A Zamfara – Gwamna Matawalle

  Gwamnan Zamfara Bello Muhammad, Matawallen Maradun, ya ce babu ranar buɗe layukan sadarwa a jiharsa. A ranar juma'a wa'adin da gwa...

 


Gwamnan Zamfara Bello Muhammad, Matawallen Maradun, ya ce babu ranar buɗe layukan sadarwa a jiharsa.

A ranar juma'a wa'adin da gwamnan ya ɗiba na buɗe layukan ya cika, kuma a hirarsa da BBC ya ce babu ranar dawo da layukan sadarwar a jihar.

"Dole mu tsawaita don burinmu tabbatar da tsaron al'ummarmu," in ji gwamna Matawalle.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da tattaunawa da jami'an tsaro, kuma makomar tattaunawar ce za ta tantance lokacin da za a buɗe layukan, ko za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Fiye da mako biyu kenan da al'ummar Zamfara ke rayuwa babu hanyoyin sadarwa a faɗin jihar, matakin da hukumomi suka ce sun ɗauka domin ƙoƙarin magance matsalolin ƴan bindiga masu kai hare-hare da satar mutane a jihar.

Matakin toshe layukan na sadarwa ya shafi yankunan jihar Katsina da ke makwabtaka da jihar Zamfara.

Gwamna Matawalle ya kuma yi kira ga jihohin da ke makwabtaka da jiharsa da su ma su ɗauki matakin toshe kafofin sadarwa a jihohinsu, inda yake ganin hakan na ɗaya daga cikin hanyoyin kawo karshen bala'in 'yan bindiga a yankin.

Ya ce yana magana da gwamnonin jihohin da ke maƙwabtaka da Zamfara kan ɗaukar matakin toshe layuka a jihohinsu.

Matawalle ya ce sun ga alfanun toshe layukan domin a cewarsa toshe hanyoyin sadarwar, shi ya taimaka wajen kuɓutar da ɗaliban makarantar Ƙayar Maradun daga hannun 'yan bindiga a ranar Lahadin da ta gabata.

Azabar yunwa ta sa ƴan bindiga na cin ɗanyar kuɓewa

Gwamna Matawalle ya yi ikirarin cewa tun toshe hanyoyin sadarwa da aka yi a faɗin Zamfara "babu wani babban abin da ya faru," yana mai cewa "ƴan bindiga sun koma suna yi wa wadanda suka sace bulala a madadin kuɗin fansa da suka rasa."

Ya kuma ce azabar yunwa ta sa ƴan bindiga suna cin ɗanyar kuɓewa saboda sabbin matakan da aka ɗauka na toshe hanyoyin sadarwa da hana cin kasuwanni.

"Akwai wani sarki da yake ba ni bayanin cewa ƴan ta'adda sun zo bakin gari, kuɓewar da aka shuka a cikin garin duk sun yanke ta, kuma haka nan suke cinta ɗanya saboda azaba ta yunwa," in ji shi.

Al'umma a Zamfara sun daɗe suna fuskantar hara-haren tare da ƙone garuruwansu daga ƴan fashi masu ɗauke da manyan bindigogi.

Hukumomi da jami'an tsaron sun sha iƙirarin cewa suna kokarin ganin an shawo kan matsalar da magance ta baki daya, amma har yanzu ana kai hare-hare da garkuwa da mutane duk da ikirarin gwamnatin Zamfara na yin sulhu da ƴan fashin.


-BBC Hausa

No comments