Bankwana Da Malam Awwal Bauchi, Bawan Allah!

             Hoto: Malam Awwal Bauchi

Daga Mahdi Garba
 
Ranar Jumma’a 17 ga watan Safar shekara ta 1443 (24 ga watan Satumba 2021) ta zo min da wani labari mai daci, mai yanke dukkan annushuwa da farin ciki. Na dade ban ga mutuwa irin ta wannan mutumin kirkin ba, wanda ban ga sunan da ya fi dacewa da shi ba kamar, ‘Bawan Allah’. Ba wani ba ne face dattijon arziki kuma gogaggen dan jarida Malam Awwal Bauchi ba. 
 
Alakar mu da mamacin ta faro ne a wajejen shekarun 2013 ko 2014. Duk da bana iya kiyaye lokacin amma na san hakan ya faru ne sakamakon bibiyar shirye-shiryen Rediyo Hausa Iran (IRIB Hausa) da nake ne. Bayan dadewa da na yi a rayuwa ina fatan kasancewa dan jarida, ‘yan jarida na burge ni. Ba kawai haka ba, na kan yi iya kokarina na kulla zumunci da su. Sakamakon haka ne alakar mu da Malam Awwal ta faro. 
 
Daga cikin rayuwar sa akwai wasu darussa da nake ganin za mu ci moriyar rayuwar mu idan muka tasirantu da su. Daga jajircewa wajen aiki, zuwa rashin girman kai, da kuma kyakkyawar mu’amala da kowa, da kuma rikon amana, sai na ke ga babu wani bangare na rayuwarsa da idan aka duba ba abin koyi ba ne. 
 
Na dade da sanin sunan shi saboda karance-karancen littafan da ya fassara daga Farisanci zuwa Hausa da kuma bibiyan sashen Hausa na shafin jagoran kare juyin-juya hali na Iran, Ayatollah Ali Khamnei da kuma shafin Alwilyahnews (dot) net. Daga yanayin yadda ya ke fassara jawaban jagoran da kuma jawabin Sakataren Hizbullah, Sayyid Hassan Nasrullah, da zarar ya kammala kai za ka gane kawai wannan bawan Allah jajirtacce ne wajen aikin da ya sa gaba. Wata cewa ta yi, ko cikin rediyo idan ka ji yadda ya ke gabatar da shiri, kai ka san wannan salihin bawa ne. 
 
Idan kuma ta janibin girman kai ne, to ina ga marigayin bai ma san wannan dabi’ar ba, balle ma ya yi ta. Duk da shekarunsa da daukakar da Allah Ya bashi, amma idan muka fara magana kai ka ce mun taso tare ne. Kai ka ce irin abokan juna muke. Musamman a shafin sadarwa na WhatsApp, da zarar na dora wani abu na ban dariya haka, ko shi ya dora (a status), sai ka ji mun kaure da dariya. Daga nan kuma sai ka ji mun fara hira. Shi babu ruwan shi. 
 
Ina girmama shi sosai, kuma ni ma na lura yana gani na da girma, duk da kuwa shekarunsa sun ninka nawa. Amma shi ko a kwalar rigarsa, bawan Allah. 
 
Hirarrakin mu mafi yawan lokuta suna karkata ne kan addini, al’ada, siyasar gabas da tsakiya kuma zamantakewa. 
 
Bana manta yadda shekarar da ta wuce muka yi hira kan yadda matasa suke kallon shirin ‘Big Brother Naija’ da ake haskawa a akwatin DSTv. Ya koka sosai kan yadda shirin ke lalata tarbiyar matasa da su kuma yadda matasan suka mayar da hankali wajen kallon shirin. 
 
Hirar mu kuwa mai wuyar katsewa sai kan marigayi Dakta Mamman Shata. Tun da ina son marigayin mawakin, kuma shi ma Malam Awwal yana son shi da wakokinsa, sai mu dade mu na hira kan Mamman Shata. 
 
Akwai wata rana muna hira sai na tambayeshi ya taba ganin Dakta Shata, sai ya ce, ai shi ba sau daya ba ma. Ya kuma ce min, “Last (karshen) ganinsa da na yi shi ne lokacin Abacha, lokacin da Gaddafi ya zo Nigeria suka zo Kano da Abacha, to lokacin mun je gidan sarki Ado Bayero a nan ma na gan shi ya zo tare da tawagar Dan Kabo gidan sarkin.” 
 
Hirar mu ta karshe da shi ranar Jumma’a 30 ga watan Yuli ne. Ya tambaye ni kan matakin da nake kan wani abu da nake, na kuma ba shi amsa. Can kuma sai na ga ya cillo min sakon, “Ina taya junanmu murnar sake Malam, Allah Ya kara masa lafiya,” nan ma na ba shi amsa. 
 
A fannin mu’amala da jama’a ta yau da kullum, sai na lura irin yadda na ke yaba masa haka kowa ke yaba wa Malam Awwal. Mu’amalarsa kyakkyawa ce da kowa, har wadanda suke saba a fahimta. Yana girmama matsayar jama’a, kuma yana mutunta su. Shi ya sa tun bayan sanar da rasuwarsa a jiya, duk wanda ya san shi, cikin alhini ya ke. 
 
A janibin rikon amana kuwa, wadanda suka yi hulda da shi, musamman ta bangaren kudi sun shaide shi a matsayin mutum mai kiyaye haram. Babu cuta, balle cutarwa a mu’amalamarsa. 
 
Allah Ya gafarta wa Malam Awwal Abubakar Bauchi, Ya kula da iyalansa, Ya kuma ba makusanta hakurin jure wannan gagarumin rashin albarkacin Manzon Allah da iyalansa tsarkaka. 
 

Post a Comment

0 Comments