![]() |
Jami'an Kwastam na kokarin hana kar a dauke su hoto. |
Bayan
Rahoton da wannan Jarida ta MADOGARA ta wallafa na yadda Jami’an Hukumar
Kwastam suka budewa tawagar Kwamishinan Kananan Hukomi da Harkokin Masarauta ta
jihar Katsina wuta a daidai garin Mai Adua daga Daura a ranar Talata, Hukumar Kwastam
ta kafa wani kwamiti da zai binciki harbin da aka yi a tawagar Kwamishinan.
Karanta labarin a nan; YANZU-YANZU: Jami'an Kwastam Sun Budewa Kwamishina Wuta A Katsina
![]() |
Kwamishinan, Alhaji Ya'u Umar Gwajo Gwajo |
Dalha
Wada-Chedi shi ne Kwanturola na Hukumar ta Kwastam ta jihar Katsina ya bayyana
wa manema labarai cewa wannan Kwamandan da ake zargi shi ne ya budewa tawagar
wuta an kafa kwamitin binciken akan sa dangane da faruwar lamarin.
Ana
zargin Jami’in Kwastam din da harbi a jerin gwanon na Kwamishinan a yayin
gudanar da aikinsu akan hanyarsa ta dawowa daga Karamar Hukumar Daura zuwa
gidansa dake Mai-Adua.
Wada-Chedi
ya bayyana cewa yana fata kwamitin zai yi aikinsa bisa adalci, ya kara da cewa
kwamitin da aka kafa za a gabatar da shi ga jama’a da kuma daukar matakin da ya
dace.
Kalli hotunan yadda aka kai harin; Yadda Jami'an Kwastam Suka Bude Wa Kwamishinan Kananan Hukumomi Wuta A Katsina Cikin Hotuna
0 Comments