Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ƴan ƙabilar Igbo ne ke ke juya tattalin arzikin Najeriya. Yayin wata ziyarar ƙaddamar da ayyuka da s...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ƴan ƙabilar Igbo ne ke ke juya tattalin arzikin Najeriya.
Yayin wata ziyarar ƙaddamar da ayyuka da shugaban ƙasar ya kai jihar Imo, ya shaida wa dattawan yankin cewa mutanensu sun bazu zuwa yankunan kasar da dama tare da zuba jari a harkokin kasuwanci daban-daban.
''Daɗina da ƴan ƙabilar Igbo shine babu inda za ka sa ƙafa a Najeriya ba tare da ka ga su ke jan ragamar harkokin kasuwancin yankin ba'' inji Buhari.
Tun da farko ƙungiyar ci gaban al'umma yankin ta Ohaneze Ndigbo ta shaida wa shugaba Buharin ƙorafinta na cewa ba a damawa da al'ummar yankin a gwamnatinsa.
No comments