Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gidaje miliyan 1.6 da ƴan Najeriya miliyan takwas ne ke amfana da tallafin kudi da gwamnatinsa ke bay...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gidaje miliyan 1.6 da ƴan Najeriya miliyan takwas ne ke amfana da tallafin kudi da gwamnatinsa ke bayarwa domin rage raɗaɗin talauci.
Cikin sanarwar da fadar shugaban ta fitar a ranar Talata, Buhari ya ce ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi na rage talauci a Nijeriya na ci gaba da bunƙasa kamar yadda BBC Hausa ta labarto.
Sanarwar ta ce Buhari ya faɗi haka ne a bikin buɗe taron shekara-shekara na harkokin banki da kuɗi na cibiyar horar da ma’aikatan banki ta Nijeriya.
A cikin jawabinsa a cewar sanarwar, shugaban ya ce rajistar talakawa da aka yi da marasa galihu ta ƙunshi mutum miliyan 32.6 daga gidaje miliyan 7 na masu ƙaramin ƙarfi.
Ya kuma roƙi bankuna su taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwarsu.
No comments