Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da kwamishinonin hukumar zaben kasar guda 3 inda ya bukace su da su jajirce wajen bada gudumawar...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da kwamishinonin hukumar zaben kasar guda 3 inda ya bukace su da su jajirce wajen bada gudumawar tabbatar da zabe mai inganci a cikin kasar.
Kwamishinonin na daga cikin wadanda Majalisar Dattawa ta amince da nadin su a watannin da suka gabata.
Daga cikin su akwai Farfesa Muhammad Sani Adam wanda ke wakiltar Yankin Arewa ta Tsakiya da Dr Baba Bila dake wakiltar Arewa ta Gabas sai kuma Farfesa Abdullahi Abdul dake wakiltar Arewa ta Yamma.
Bikin rantsuwar ya gudana ne kafin taron mako-mako na majalisar ministocin kasar da aka saba gudanarwa kowacce ranar laraba a fadar shugaban kasar.
Cikin wadanda suka halarci bikin rantsuwar harda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Gida Mustapha da ministan shari’a Abubakar Malami.
Ana saran kwamishinonin su bada gudumawa wajen shirin zaben shekarar 2023 da zai gudana.
No comments