Buhari Ya Shilla Kasar Amurka Taron Majalisar Dinkin Duniya

 

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja a yau Lahadi zuwa New York domin halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA76) na 76.

Zaman zai fara ne daga ranar Talata, 14 ga watan Satumba.

Taken taron na UNGA na wannan shekara shi ne: "Gina Tsarin Rayuwa mai cike da Fata-Don Warkewa daga COVID-19, Sake Ginawa Mai Dorewa, Amsa Buƙatun Duniya, Girmama Haƙƙin Mutane da Rayar da Majalisar Dinkin Duniya."

Shugaban na Nijeriya zai yi jawabi ga Majalisar a ranar Juma'a, 24 ga watan Satumba inda zai yi jawabi kan jigon taron da sauran batutuwan da suka shafi duniya.

Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban, shi ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar inda ya ce Shugaba Buhari da mrmbobin tawagarsa za su kasance cikin wasu muhimman tarurruka.


Post a Comment

0 Comments