RFI Hausa ta labarto cewa; Hukumar Yaki da cututtuka a Najeriya tace sake dawowar annobar korona zagaye na 3 na matukar illa a cikin kasar...
RFI Hausa ta labarto cewa; Hukumar Yaki da cututtuka a Najeriya tace sake dawowar annobar korona zagaye na 3 na matukar illa a cikin kasar, sakamakon mutuwar mutane 49 a rana guda, yayin da aka gano mutane kusan 1,000 da suka harbu da cutar.
Wannan adadi da Hukumar ta gabatar ya nuna cewar ya zuwa wannan lokaci mutane 2,544 da cutar ta kama suka mutu a Najeriya, abinda ke tabbatar da sake dawowar ta.
Sakamakon sabbin alkaluman da aka samu daga jihohin Najeriya ya nuna cewar adadin mutanen da bincike ya nuna sun harbu da cutar ya kai 195,052, kuma daga cikin su sama da 2,500 sun mutu.
Sabbin alkaluman sun nuna cewar a Jihar Lagos kawai an samu mutane 456 da suka harbu da cutar a karshen mako, sai Jihar Ondo mai mutane 180, Edo na da mutane 66, sai kuma Rivers mai mutane 62.
Hukumar ta kuma bayyana cewar an samu sabbin mutanen da suka kamu da cutar 26 a Jihar Niger, 25 a Akwa Ibom, yayin da aka samu 22-22 a Jihohin Ekiti da Kwara da kuma Oyo.
A makon jiya Hukumar yaki da cutar a Najeriyar ta bayyana shirin tilastawa Yan kasar karbar maganin rigakafi domin yaki da cutar, yayin da Jihohin Edo da Ondo suka bayyana irin wannan shirin na tilastawa jama'a karbar allurar.
No comments