Gwamnatin jihar Katsina ta ce zuwa yanzu mutane sama da 150 aka tabbatar mutuwarsu daga cikin wasu akalla dubu 5 da 677 da suka kamu da cu...
Gwamnatin jihar Katsina ta ce zuwa yanzu mutane sama da 150 aka tabbatar mutuwarsu daga cikin wasu akalla dubu 5 da 677 da suka kamu da cutar Kwalara, tun bayan barkewar a jihar kimanin wata guda da ya gabata.
Babban Sakataren Hukumar Kula da Kula da Lafiya a matakin Farko a Katsina, Dakta Shamsudeen Yahaya, ya shaidawa manema labarai cewa, an tattara alkaluman ne daga asibitoci da sauran cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko da ke jihar.
Jami’in ya kuma bayyana fargabar adadin wadanda suka mutu na iya zarta wanda aka kididdige, kasancewar akwai mutane da dama musamman a karkara, da ba sa zuwa asibiti.
A farkon watan Agusta hukumomin jihohin Sokoto da Zamfara suka sanar da mutuwar mutanen da yawansu ya kai 53, 30 daga cikin su Zamfara, yayin da 23 suka mutu a Sokoto.
No comments