Daga Wakilinmu Da safiyar yau Litinin ne aka samu fashewar tankar man fetur a babban Birnin Yola ta jihar Adamawa. Ya zuwa yanzu babu tabb...
Daga Wakilinmu
Da safiyar yau Litinin ne aka samu
fashewar tankar man fetur a babban Birnin Yola ta jihar Adamawa.
Ya zuwa yanzu babu tabbacin ko an
rasa rai ko jikkata a fashewar tankin man fetur din. Lamarin dai ya auku ne a
daidai PZ Roundabout dake titin Airport.
Majiyarmu ta labarto mana cewa
tankar man fetur din na kamfanin Conoil ne, ta kuma fadi ne a daidai lokacin da
direban ke kokarin juyawa a roundabout
din.
Ababen hawa da shaguna da dama dake
tsawon mita 80 a tsakanin inda tankar man fetur din ta fadi sun kama da wuta,
wanda hakan ya jawo asarar da har ya zuwa hada rahoton nan ba a tantance ba.
Ya zuwa hada rahoton nan gamayyar
masu kashe wuta na jiha da gwamnatin Tarayya sun isa wurin domin kashe wutar. Kazalika
a gefe guda kuma, sojin sama da Kamfanin Faro sun isa wurin suna taimakawa
wajen kashe wutar.
No comments