Dakarun Nijeriya da suka hadar da sojoji da kuma 'yan sanda sun kashe wasu 'yan bindiga a kauyen Alawa da ke yankin Shiroro a Jiha...
Dakarun Nijeriya da suka hadar da sojoji da kuma 'yan sanda sun kashe wasu 'yan bindiga a kauyen Alawa da ke yankin Shiroro a Jihar Neja kamar yadda BBC ta labarto.
Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa dakarun hadin gwiwar sun yi wa 'yan bindigar kwantan bauna ne, wadanda ke kokarin tserewa aikin da sojojin Najeriya ke yi a jihar Zamfara.Wata majiya ta kuma shaida wa jaridar cewa yayin wannan dauki ba dadi an kashe soja guda da kuma wasu da suka ji raunuka."Dakarun sun samu rahoton sirri na fitowar 'yan bindigar daga Zamfara sun nufin kauyen Alawa.
"Sun tsallake wasu wurare da sojoji suke bincike a cikin dazuka, amma mun samu damar far musu a Manganda. a kalla an kashe mutum 42 daga cikin su da yawa sun tsere da ciwuka a jikinsu.
"An kashe mana soja daya, an kuma dauki sauran mutanenmu da suka jikkata zuwa Asibitin Asma'u da ke Kagara.
"Mun kwace wasu makamai da babura da dai wasu abubuwa masu yawa, in ji wannan majiyar tasu.
No comments