Daliban Jami’ar ABU Zariya Sun Yi Sabon Shugaba

 


Daga Fatima Idris, Zariya

A ranar 30 ga watan Agustan 2021 aka gudanar da zaben sabbin shugabanni bayan cikar wa'adin wanda suke kai a baya.

Zaben an gudanar da shi ne a filin Kwantagora dake harabar Jami'ar. Shi ne mukami mafi girma ta dalibai.

A zaben na wannan lokacin, mutum bakwai suka fafata domin neman shugabancin kujerar.

An fitar da kuri'u guda 79 cikin ikon Allah Dalibi mai suna Jibrin Idris daga jihar Zamfara a Tsangayar Ilmin Kimiyyar kasa (Science Education Geography), inda ya sami nasarar cinye zaben bayan kada mutane 6 da samun kuri'u 27 wanda hakan ya ba shi damar zama shugaban daliban Jami'ar na Ahmadu Bello Zariya baki daya.

Farfesa Ibrahim Dabo daga sashen Kimiyyar Sinadarai shi ya shugabanci zaben kuma ya shaidawa manema labarai cewa ya ji dadin yadda daliban suka bi dukkan sharudan zaben kuma ya yi fatan alheri gare su.

Kwamared Jibril zababben shugaban ya bayyana jin dadinsa bisa yadda dalibai suka bashi goyan baya.

Kuma ya yi alkawari zai cikawa dalibai dukkan alkawarin da ya dauka kuma ya ce zai kare masu hakkokinsu.

Karshe ya yi kira da hukumar tsaro na Jami’ar da su dage wajen kare rayukan dalibai kamar yadda suka saba.


Post a Comment

2 Comments

  1. Hi my name is Aminu Bundu please I'll like to reach out the management

    ReplyDelete