Dalilan Da Ya Sanya Na Kai Karar Mahaifiyata Wajen EFCC -Abdul'azeez Ganduje


Daga Munira Muhammad

Babban dan Gwamnan jihar Kano, Abdul'aziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Dr Hafsat Ganduje a gaban hukumar yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa wato EFCC akan zargin da yake yi mata da almundahana da kuma azurta kanta ta hanyoyin da yake ganin ba su dace ba.

Tuni dai a bangaren Hukumar EFCC din ta aikewa da Dr Hafsat Ganduje mai dakin Gwamnan Kano da goron gayyata domin ta je gaban Hukumar don amsa tambayoyi kan zargin da dan na ta ke yi mata, amma ta ki amsa gayyatar ba tare da kuma ta bayar da wani uzuri a rubuce ba. 

A cikin wasikar da Abdul'aziz Ganduje ya aikewa da EFCC, ta shafi badakalar filaye da kuma miliyoyin kudade. Sai dai Kakakin Hukumar EFCC Wilson Uwujaren bai ce uffan ba dangane da batun bayan an yi masa tambaya a kai. 

Idan ba a manta ba, a baya an zargi Gwamnan Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje da yin badakala ta sama da dalar Amurka miliyan biyar, inda aka nuno shi a wani faifan bidiyo yana sunkuma dalar Amurka daga cikin kudaden 'yan kwangila, sai dai Gwamnan ya karyata bidiyon tare da kai karar jaridar Daily Nigerian da mawallafinta Jaafar Jaafar gaban kotu game da batun bidiyon Dala.

Post a Comment

0 Comments