Rfi Hausa ta labarto cewa; ana ci gaba diga ayar tambaya tun bayan gudanar da babban taron manema labarai a makon jiya wanda Kwamitin Da...
Rfi
Hausa ta labarto cewa; ana ci gaba diga ayar tambaya tun bayan gudanar da
babban taron manema labarai a makon jiya wanda Kwamitin Dattawan Jam’iyyar APC,
reshen jihar Filato ta Najeriya ya shirya don bita kan sha'anin tsaro, inda ake
neman bayani akan wasu matasa 300 da tsohuwar gwamnatin jihar ta tura Isra'ila
domin samun horo.
A
yayin gudanar da taron a ranar 3 ga watan Satumba, kwamitin ya bukaci Gwamnan
jihar Simon Lalong da ya sake nazartar badalakar daukar wasu matasa aikin
tsarom da tsohon Gwamnan jihar Jonah Jang ya yi tare da tura su Isra’ila domin
samun horo.
A
zamanin mulkinsa, an ruwaito cewa, Jang ya dibi matasa 300 tare da tura su
Isra’ila don ba su horo kan tsaro, amma tun bayan dawowarsu, har yanzu ba a ji
duriyarsu ba.
Bayanai
sun ce, akasarin matasan ‘yan kabilar Birom ne, wato kabilar tsohon Gwamnan,
kuma an yi zargin cewa, ya dibe su ne domin cimma wata manufa ta murkushe
abokan gaba a jihar amma ba don masalahar al'umma ba.
Jang
ya mulki jihar Filato a tsakanin shekara ta 2007 zuwa 2015, yayin da a zamaninsa
aka samu asarar dubban rayukan jama’a da kuma salwantar kadarori na biliyoyi a
rikice-rikicen kabilanci.
Tsohuwar
gwamnatin Jang ta PDP ta hakikance cewa, domin tabbatar da tsaro a jihar ta
samar da rundunar matsan a wancan lokaci.
Yanzu
haka kwamitin dattawan APC ya bukaci Gwamna mai ci da ya lalubo wadannan matasa
domin amfani da su wajen samar da tsaro a jihar, lamarin da ya zafafa muhawara
kan lamarin.
Wannan
muharawa dai, ta tayar da sabuwar kura a jihar ta Filato wadda ke cika shekaru
20 da fara mummanar tashin hankalin da ya haifar da rasa dimbin rayuka ranar 7
ga watan Satumabr shekarar 2001 a karkashin mulkin tsohon Gwamna Joshua Cibi
Dariye.
An
dai gudanar da taron manema labaran ne ganin yadda lamurran tsaro suka kara
sukurkucewa a baya-bayan nan jihar ta
Fliato.
No comments