Dele Alli Ya Yi Wa Mourinho Fata-fataDan wasan tsakiya na Tottenham, Dele Alli ya caccaki Mourinho. Dele Alli ya ce tsohon kocinsa Jose Mourinho ya cika mayar da hankali a kan abokan hamayya a yayin shirye shiryen tunkarar wasa a maimaikon ya yi abin da ya fi dacewa.

Alli bai samu jituwa da Mourinho ba a lokacin da kocin dan kasar Portugal ke horar da Tottenham.
Sai dai yanzu dan wasan ya zama mai murza leda a koyaushe a karkashin mai horarwa, Nuno Espirito Santo.

Dan shekara 25 din ya kasance cikin ‘yan wasan tsakiya da ake damawa da su a tsakiyar filin Tottenham a wannan zamani na Koch Nuno, kuma ya buga ilahirin wasannin gasar Firimiyar Ingila na wannan kaka tun da aka fara.

Alli ya shaida wa manema labarai cewa Mourinho yana da dabi’ar daukar lokaci yana nazari a kan abokan hamayya, maimakon ya mayar da hankali a kan abin da ya dace a yi.


Post a Comment

0 Comments