Gwamnonin kudancin Najeriya sun ce dole ne shugaban kasa ya fito daga kudancin kasar a zaben shekara ta 2023. A wani taro da suka gudanar ...
Gwamnonin kudancin Najeriya sun ce dole ne shugaban kasa ya fito daga kudancin kasar a zaben shekara ta 2023.
A wani taro da suka gudanar a jihar Enugu, gwamnonin sun jaddada wasu yarjejeniyoyi da suka cimma wanda Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu, shugaban kungiyar gwamnonin ya ambato a wata sanarwa.
Yarjeniyoyin sun haɗa da buƙatar gwamnonin yankin ta ɗan yankin ya zama shugaban Najeriya a 2023 da jaddada buƙatarsu ta shigar da gyaran da suke so a yi a kundin tsarin mulki da batun hana kiwo da batun harajin VAT.
Akeredolu ya ce "gaba ɗaya gwamnonin yankin mun amince da cewa dole ne shugaban ƙasa na gaba a Najeriya ya fito daga yankin Kudu. Sai dai kawo yanzu ba mu tsayar da mutum ɗaya da zai fito a zaɓen 2023 ba."
Kan batun hana kiwo, kungiyar gwamnonin ta ce ta gamsu da yadda jihohin kudancin Najeriya ke kawo gyara cikin dokokin kiwo a fili kuma Gwamna Akeredolu ya ce sun buƙaci sauran jihohin yankin da ba su sa dokokin hana kiwon, su yi hakan.
Haka kuma, ya ce jihohin yankin na da ƴancin kafa harajin VAT da ake samu daga jihohin da aka sayar, lamarin da ya janyo jayayya tsakaninsu da gwamnatin tarayya.
-BBC Hausa
No comments