Wanne Hali Jihar Zamfara Take Ciki? Daga Abidi Aminu Bua Kamar yadda hukumar jihar Zamfara tare da haɗin gwiwar ma'aikatar ...
Wanne Hali Jihar Zamfara Take Ciki?
Daga Abidi Aminu Bua
Kamar yadda hukumar jihar Zamfara tare da haɗin gwiwar ma'aikatar kula da sadarwa ta ƙasa (NCC) ta katse hanyoyin sadarwa a faɗin jihar, a matakinta na daƙile matsalar rashin tsaron da jihar ke fama da ita a makonni biyu da suka shuɗe.
Abin tambayar a nan shi ne; shin an samu ci gaba a harkar tsaro kamar yadda gwamnati take iƙirari? Wanne hali ƴan'uwanmu na jihar Zamfara suke ciki?
Haƙiƙanin gaskiya ci baya yafi yawa akan ci gaban da aka samu a tsawon wannan makonni biyun, domin hare-haren ƴan ta'addan ya yawaita fiye da kwanakin baya, rashin imanin su ya ƙara bayyana a fili, haka kuma al'ummar jihar suna cikin halin fargaba da takura fiye da sauran lokutan baya.
Yanzu salon ƴan ta'addan Zamfara da aka fi sani da ɓarayin shanu ya canza baki ɗaya, domin a sati biyun nan a iya binciken da na yi ban samu labarin sun yi garkuwa da wani ba, abin da suke yi shi ne kawai kai hare-hare a ƙauyuka tare da kisa kan mai uwa da wabi.
A ranar Lahadi 12 ga wannan watan na Satumba a garin Kwanar Kalgo mai nisan kilomita 10 da garin Talata Mafara ɓarayi sun shiga cikin dare suka yanka wani gawurtaccen ɗan sa kai, abin da ya fusata ƴan sa kai ɗin suka kashe duk wani Bafullatani da aka gani a yankin, tare da tare na kan hanya ko da bai ji ba bai gani ba.
A ranar 14 ga watan Satumba ma sun hallaka sojoji 23 a wani ƙauye da ake kira Ɗan Sadau da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Maru.
A ƙaramar hukumar Zurmi akwai wani gari Moriki, ɓarayi aka samu sun shiga tirela suna nufin guduwa, sojoji suka kashe su, su kuma suka yi wa sojojin kwanton ɓauna suka hallaka adadin da ba a tantance ba.
Haka zalika, a satin da ya gabata sun hallaka sojoji 18 a Ƙaramar Hukumar Shinkafi, haka ma akwai wani ƙauye a yankin da suka shiga suka kashe Dattijai 32 suna salla!
A ƙauyen Raƙuma mai nisan kilomita 8 da garin Talata Mafara kuma, abin ya munana, inda suka shiga ranar 18 ga Satumba suka bude wuta har zuwa yanzu ba a gama tantance adadin mutum nawa ya rasa ransa ba, zuwa lokacin da na baro yankin an yi jana'izar mutum 36.
Haka kuma a ranar 19 ga Satumba sun kai mummunan hari a wani ƙauye yankin Maru, suka hallaka mutum 23.
Ɓangaren ƴan uwanmu na Zamfara kuma, lallai al'umma suna cikin yanayin matsi da takura mafi muni a tarihin jihar Zamfara, saboda wasu dokokin da gwamnatin ta saka ba tare da duba zuwa ga halin da talakawanta za su shiga ba.
An hana cin kasuwanni a faɗin jihar baki ɗaya, saboda haka ba batun samun abin kai wa baka, an hana shiga ko fita da abinci ballantana mu na waje mu kai wa ƴan'uwanmu ɗaukin abinci, kuma gwamnati ba ta ba su abin da zai rage wannan raɗaɗin ba, kai musamman ma aka saka 'checking point' na 'yan sanda da Alƙali a mashigar kowacce ƙaramar hukuma, idan har aka ganka da tiyar abinci (gero, dawa, masara, shinkafa, wake, alkama da sauransu) to za a cika tara dubu ashirin da sunan daƙile isar abinci ga ɓarayi!
Babban abin tsoro shi ne an rufe hatta da bankuna, babu damar turawa ɗan uwa kuɗi ko cirewa, ba sau ɗaya ba ana bani ATM Card na je Sokoto na ciro kuɗi saboda a Zamfara Bankuna basa aiki.
Idan ka zubawa mashin man fetur da ɗan dama, za a tsiyaye man a yi maka tara dubu biyu.
Al'umma babu harkar yi, babu wani tallafi daga gwamnati.
Akwai matasa sun fi a ƙirga waɗansa na sani na ga sun gudo daga yankin zuwa jihar Sokoto domin neman abin kai wa baka!
Wasu masu hali ne, amma a cikin sati biyun nan sun talauce, ko abincin da za a ci gidansu ya gagare su, alhali kafin yanzu har ɗawainiyar wasu su suke ɗauka.
Wannan shi ne a taƙaice halin da dangi, ƴan uwa da abokan arziki na Jihar Zamfara suke ciki.
Dan Allah ku yaɗa wannan rubutun domin duk mai ɗan uwa a Zamfara ya san halin da suke ciki domin kai masu ɗauki.
23 ga Satumban, 2021.
No comments