Shugaban Rundunar Sojin Nijeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya Daga Wakilinmu Da Rahoton Leadership Hausa Rahotannin da MADOGARA ta samu n...
![]() |
Shugaban Rundunar Sojin Nijeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya |
Daga Wakilinmu Da Rahoton Leadership Hausa
Rahotannin da MADOGARA ta samu na nuni da cewa a makonnin da suka gabata ne aka wayi gari rundunar Sojin Nijeriya suka dira a gonakin mutanen Gyallesu da Tudun Wada dake karamar Hukumar Zariya ta jihar Kaduna, inda suka girbe shukokinsu da ta riga ta yi yabanya a gonakinsu dake jikin Barikin Sojojin ta DEPOT. Lamarin da ya fusata masu gonakin tare da Allah-wadai da abin da sojojin suka aikata musu.
Fiye da shekara biyu da suka gabata,
wasu manoma da suke yankin Gyallesu da Jushin Waje da Tudun Wadan Zariya suka
shigar da kara a babbar kotun daukaka kara da mai Shari’a Kabiru Dabo ke
shugabanta, kan yadda mahukuntan Barikin sojoji wato DEPOT dake Sabon Garin
Zariya suka hana ci gaba da noma a gonakinsu kamar yadda majiyarmu ta labarto.
Bayan kotun ta saurari wannan kara
na al’ummomin da aka ambata, ta bayar da umurni a rubuce ga manoman da suka kai
karar cewar, kotu ta amince su ci gaba da noma gonakinsu, yayin da kuma za a ci
gaba da shari’a a kan kukan da manoman suka kai Barikin sojojin.
A farkon damunan wannan shekara,
manoman sun bi umrnin wannan babbar kotu, inda suka ci gaba da noma a gonakinsu
kamar yadda suka saba a duk shekara. Kwatsam sai wasu sojoji daga wannan bariki
na DEPOT suka ba su umurni a kan su dai na shigan gonakin da sunan noma, in ba
haka ba za su dauki matakin da za su yaba wa aya zaki.
Mai magana da yawun manoman, Alhaji
Musa Ibrahim Gyallesu ya shaida wa wakilinmu cewar, sun rubuta takardar koken
hana su noman, inda suka kai ga mahukumtan Barikin Sojojin, amma ba su dauki
matakin da suka bukata ba na a barinsu su ci gaba da noma a gonakinsu kamar
yadda babbar kotun ta bayar da umurni.
A game da matsalolin da suke
fuskanta kuwa, Alhaji Musa Gyallesu ya shaida wa wakilinmu cewar bayan sojojin
sun hana su noma, lokacin da amfanin gonan da suka noma ta yi yabanya mai kyau,
sai sojojin suka yi feshi a daukacin gonakin, inda suka kashe dukkanin abubuwan
da manoman suka shuka.
Alhaji Musa Ibrahim Gyallesu ya ce
sun rasa abin da za su ci tare da iyalansu kuma babu wata sana’ar da suka
dogara da ita, sai wannan sana’a ta noma.
Alhaji Musa ya kuma shaida wa
wakilinmu cewar sun gaji wadannan gonaki ne daga Kakanninsu ya zuwa iyayensu,
inda ya ce sun mallaki wadannan gonaki fiye da shekara 100 suka gabata.
No comments