EFCC Ta Ce Shugabanta Ya Warware Kuma Yana Cikin Koshin Lafiya

 


Hukumar EFCC a Nijeriya ta ce shugabanta Abdulrasheed Bawa ya warware kuma yana cikin koshin lafiya.

Abdulrasheed ya kasance cikin yanayi na jiri a lokacin gabatar da jawabi a wajen wani taro a fadar shugaban kasa a jiya Alhamis.

Da farko jaridun Najeriya sun rawaito cewa yana bayyani ne kan wani mutum da aka kama da layukan waya 116 yana damfarar mutane, lokacin da ya soma jin jiri.

Jaridun sun kuma shaida cewa daga nan aka yi awon gaba da shi zuwa asibiti.

Ministan sadarwa Dr Isa Ali Pantami na cikin wadanda suka taimaka masa lokacin faruwar lamarin

EFCC dai ba ta yi karin haske kan abin da ya sa Bawa ya shiga yanayin rashin lafiya ba, a sanarwar da ta fitar


Post a Comment

0 Comments