Daga Wakilinmu Bayan ikirarin da Hukumar leken asiri ta kasa, NIA ta yi na cewa ba ta rike da Fasfo din fita kasashen waje na Shaikh Ibrah...
Daga Wakilinmu
Bayan ikirarin da Hukumar leken asiri ta kasa, NIA ta yi na cewa ba ta rike da Fasfo din fita kasashen waje na Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa, Malama Zeenat Ibraheem, Harkar Musulunci a Nijeriya ta kammala shirye-shiryen neman sabbin takardun kamar yadda Jaridar Punch ta labarto a ranar Litinin.
Tuni aka kammala cimma matsayar tunkarar Hukumar shige da fice ta Nijeriya (NIS) domin ganin an sabunta Fasfo din fita kasashen wajen wanda aka kai matakin nasara a cewar rahoton.
Lauyan
Shaikh Zakzaky, Marshal Abubakar, wanda yake Babban Lauya ne a Ofishin Femi
Falana (SAN), a tattaunawar da aka yi da shi, ya bayyana kwarin guiwar da suke
da shi na cewa za su samu nasarar ganin an sabunta Fasfo din fita kasashen
wajen saboda; “hakkinsa ne ya mallaki Fasfo din”, inji shi.
Ya ci gaba da cewa; “Mun rubutawa Shugaban Hukumar Shige da Fice; za mu je ofishin fasfo din domin karbar sabo. Hukumar NIA ta ce fasfo din baya tare da su. Muna da takardar rantsuwa da ta 'yan sanda; za mu je kawai mu samo sabuwa daga Hukumar Shige da Fice. Za mu yi hakan a gobe (a jiya Laraba) ko kuma jibi (a yau Alhamis)”.
Da aka tambaye shi ko yana da tabbaci kwarin guiwar za su ba su wani, Marshal ya ce, “Za su bayar; hakkinsa ne ya sami fasfo. Su (NIA) sun ce ya bata; suna da shi amma sun ce ba ya tare da su. Wannan yana nufin, ya É“ace; don haka, za mu nema kuma mu sake samun sabo. ”
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa korafin da Academic Forum na Harkar Musulunci da kuma Babban Lauyan kare hakkin bil’adama, Femi Falana (SAN), suka yi bisa kin amincewar gwamnati ta saki takardun tafiya na Shaikh Zakzaky da matarsa, ya sanya NIA suka ce takardun ba ya hannunsu.
Ma’auratan ba su samu sun tafi kasar waje neman magani tun bayan da Babbar Kotu a Kaduna ta wanke su daga dukkanin zargin laifuka tare da sakin su a karshen watan Yulin 2021.
NIA
sun ce ba ya hannunsu ne a cikin takardar martani da NIA din ta rubuta mai dauke da lamba N/OPS/14’4A/VOL.2, mai kwanan watan 12 ga Agusta wanda wani mai suna
I. Giwa ya rubuta a madadin Darakta Janar na Hukumar, Ahmed Rufai Abubakar, ya
kuma aikawa Babban Lauya a Ofishin Falana, Marshal Abubakar.
No comments