Bbc Hausa ta labarto cewa; kungiyar manyan ma'aikatan albarkatun mai a Najeriya, PENGASSAN, ta ce faÉ—uwar darajar naira kan dalar Amur...
Bbc Hausa ta labarto cewa; kungiyar manyan ma'aikatan albarkatun mai a Najeriya, PENGASSAN, ta ce faÉ—uwar darajar naira kan dalar Amurka ne makasudin karuwar farashin gas.
Farasahin gas din da ake girki a Najeriya ya karu da kusan kashi 100 a cikin watanni 8 a ƙasar, yayinda gwamnati a kwanan nan ta soma amfani da sabon tsarin harajin kashi 7.5 cikin 100 kan gas din da ake shigowa da shi ƙasar.
Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo ya shaida cewa tunda farashin gas din ana lissafinsa ne a kan dalar Amurka, kasuwar dalar za ta ci gaba da tasiri kan farashin.
Mista Festus ya ce a yanzu duk yada kasuwar dala ta kasance akan naira haka za a ke samun sauye-sauye a farashin gas a kasuwa.
Tukunyar gas mai nauyin kilo 12.5 da ake sayarwa a kan 3,500 a Disambar 2020, a yanzu ana sayar da ita a kan 6,800 a wasu sassan Abuja.
Wasu mazauna Legas kuma na cewa suna sayen gas É—in a kan naira 7,200, kuma akwai hasashen zai iya kai wa naira 10,000 zuwa Disambar wannan shekara.
Wannan yanayi da ake ciki na tsadar gas na tada hankulan 'yan Najeriya da dama musamman ganin galibi mutane sun dogara da gas domin girke-girke.
No comments