Shugaba kuma mu’assafin Jami’ar Maryam Abacha American University da Franco-British International University dake Kaduna, Farfesa Adamu Ab...
Shugaba kuma mu’assafin Jami’ar Maryam Abacha American University da Franco-British International University dake Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya tallafawa mata 100 da naira dubu hamsin-hamsin ga kowannensu.
Tallafin wanda aka bai wa wadanda suka amfana gidauniyyar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ne ta ba su bayan da suka samu horo akan sana’ar kwalliya wanda gidauniyyar ta dauki nauyi a Kano a ranar Lahadi.
Da yake jawabi a taron, Farfesa Abubakar Gwarzo, wanda har wala yau shi ne shugaban kungiyar Jami’o’i masu zaman kansu ta Afrika, ya shawarci wadanda suka amfana da su yi amfani da kudaden da aka ba su wajen kafa harkar kasuwancin da zai sanya su dogara da kawukansu, inda ya kara da cewa ‘ya’yan Talakawa suma za su iya cimma duk abin da suka yi muradi matukar sun yi amfani da damar su da suka samu.
Har wala yau ya shawarci matan da suka samu horo akan sana’ar kwalliyar da su yi iya bakin kokarinsu wajen ganin sun koyawa sauran ‘yan’uwansu mata da ba su samu wannan damar ta halartar wannan taron horaswa din ba, inda ya ce wannan hanyar ce kawai za ta ba su damar dogaro da kansu wajen ci gaban kasarnan.
Maryam Isah, daya daga cikin wadanda suka amfana da horaswar kuma aka bata naira 50, 000 daga gidauniyyar, ta ce kudin da aka ba su zai ba su damar kafa sana’ar da aka horas da su wanda ta ce dama rashin jarin fara sana’ar ne babban matsalar da ke fuskantar mafi yawan wadanda aka horas.
Kazalika, Hanan Muhammad, daya daga cikin wacce ta amfana ta yabawa Farfesa Abubakar Gwarzo bisa wannan tallafi da ya ba su, inda ta ce ba ta taba tsammanin kudin ba wacce ta ce zai taimaka wajen bunkasa sana’ar kwalliyar a yankunan da suka fito.
A na shi jawabin, Daraktan Gidauniyyar, Dr Musa Abdullahi Sufi, ya ce wannan tallafin yana daya daga cikin ayyukan jinkai na Gidauniyyar.
Ya ce Gidauniyyar ta yi nasarar tallafawa daidaikun mutane da al’umma ta hanyoyi daban-daban musamman a bangaren ilimi, lafiya, da tallafawa mata da matasa tare da samar da ababen more rayuwa a ciki da wajen jihar Kano.
Kowacce daya daga cikin mata 100 din nan an ba su shaidar halartar wannan taron tare da ba su naira dubu 50 (N50, 000) a yayin taron.
No comments