Shugaba kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University da Franco-British International University, Kaduna, Farfesa Adamu Abu...
Shugaba kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University da Franco-British International University, Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya taya dan Nijeriya, Ismai’l Abdulrashid, wanda ya zama Farfesa tun yana dan shekara 32.
Sakon taya murnar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Abubakar Gwarzo ya rabawa manema labarai a Kano ranar Talata.
Farfesa Abubakar Gwarzo, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Jami’o’i masu zaman kansu, ya ce nasarorin da matashin ya samu ya bayyana irin sakamakon jajircewa da sadaukarwa da ya yi saboda kishin da yake da shi ya sa ya ci gaba ba tare da la’akari da kalubalen ba.
Ya lurantar da cewa wannan nasarar da matashin ya samu zai zama abin karfafa ga matasan Nijeriya wadanda suke da burin ci gaba da karatunsu zuwa babban mataki.
“Tare da wannan babban nasara, matashi Isma’il Abdulrashid ba kawai ya sanya jiharsa alfahari bane ko Arewa, ya sanya dukkanin kasar ne.
“a don haka, a madadin Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Maryam Abacha American University da Franco-British International University, ina taya ka murna bisa wannan babban nasarar”, inji Farfesa Abubakar Gwarzo.
Matashi
Ismai'l Abdulrashid, wanda ya fito daga jihar Katsina, ya halarci Makarantar
Sakandaren Gwamnati ta Mani, kafin ya samu digirinsa a bangaren lissafi daga
Jami'ar Bayero ta Kano.
No comments