Hukumar gudanarwa ta Kamfanin gidan Man Fetur na AU Sarki Global ya karyata bidiyo da ake yadawa dangane da su, inda kamfanin ya ce bidiyo...
Hukumar
gudanarwa ta Kamfanin gidan Man Fetur na AU Sarki Global ya karyata bidiyo da
ake yadawa dangane da su, inda kamfanin ya ce bidiyon tsoho ne kuma tuni ma aka
warware wancan matsalar da ta afku a lokacin.
Hukumar
ta bayyana hakan ne a sanarwar da ta fitar da safiyar yau Juma’a inda suka
bayyana bidiyon a matsayin labarin kanzon kurege.
Hukumar
ta ce; “ku yi watsi da bidiyon da ake yadawa a halin yanzu a shafukan sada
zumunta inda ake nuna jami’an DPR na gabatar da ma’aikacin AU Sarki Global a
yayin da ake sayar da man fetur a Jarkoki da kuma leda”.
Sanarwar
ta ci gaba da cewa; “domin tabbatar da sahihin zance, labarin tsohon labari ne,
domin ya auku ne tun a cikin 2019 kafin lamarin tsaron da ake ciki ya ta’azzara
harma gwamnati ta bada umurnin da ake a kai yanzu”, ta tabbatar.
Sun
kara da cewa; “Gidajen Man Fetur dinmu na cika alkawura tare da kuma nuna goyon
baya ga matakan da gwamnati ke dauka wajen magance matsalar tsaron da ya addabi
jiharmu (Katsina)”.
“muna
rokon al’umma baki daya da su dakatar da yada wannan bidiyo domin bayanan dake
dauke da bidiyon ba gaskiya bane”, suka jaddada.
No comments