Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Gungun Mayakan Boko Haram Sun Shiga Dajin Rijana Ta Jihar Kaduna - Rahoto

  Rahotanni na nuni da cewa mayakan Boko Haram fiye da 200 sun fice daga sansaninsu da ke arewa maso gabashin kasar zuwa arewa maso yammaci,...

 


Rahotanni na nuni da cewa mayakan Boko Haram fiye da 200 sun fice daga sansaninsu da ke arewa maso gabashin kasar zuwa arewa maso yammaci, domin hada karfi da ‘yan bindiga.

Bayanan da kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito daga wasu majiyoyin tsaro guda 2 a Najeriyar, sun ce bangaren Boko Haram da har yanzu ke biyayya ga tsohon jagoransu Shekau ne ya tura kwamandoji biyu da mayaka 250 zuwa dajin Rijana da ke jihar Kaduna.

Daya daga cikin majiyoyin ya ce gungun mayakan na Boko Haram ne suka kitsa wasu sace -sacen da ake yi a arewa maso yammacin Najeriya a baya bayan nan, yayin da kuma suke ci gaba da horas da ‘yan bindiga wajen sarrafa manyan bindigogin harbo jiragen sama, bama-bamai da sauran muggan makamai.

Har yanzu dai ba a samu jin ta bakin rundunar sojin Najeriya da kuma gwamnatin Kaduna kan wannan al’amari ba kamar yadda RFI Hausa ta labarto.

A watan da ya gabata ‘yan bindigar suka kai hari kan Kwalejin horas da hafsoshin sojin Najeriya ta NDA da ke Kaduna, inda suka yi garkuwa da jami'i guda bayan kashe wasu.

A farkon wannan wata rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da farmaki kan sansanonin ‘yan bindiga a Jihar Zamfara da ke makwabtaka da Kaduna, bayan da aka katse hanyoyin sadarwa a wani mataki na dakile hanyoyin da ‘yan bindigar ke samun bayanai kan ayyukan sojin.

No comments