Gwamna Dr Ganduje a Hagu tare da matarsa, Farfesa Hafsat Ganduje Daga Auwal Adam A daidai lokacin da Babban Dan Gwamna Dr Abdullahi Umar...
![]() |
Gwamna Dr Ganduje a Hagu tare da matarsa, Farfesa Hafsat Ganduje |
Daga Auwal Adam
A daidai lokacin da Babban Dan Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje,wato Abdul’aziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Farfesa Hafsat Ganduje gaban Hukumar yaki da rashawa, EFCC kan zargin da yake yi mata da almundahana da kuma azurta kanta ta hanyoyin da yake ganin ba su dace ba, a yau Talata, AbubakarAminu Ibrahim, mai tallafawa Gwamnan Abdullahi Ganduje kan kafofin sadarwa na zamani ya wallafa hotunan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje OFR, da Uwargidansa Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje da sauran iyalansa a lokacin da suka halarci bikin yayen Dalibai wanda ya hada da Dan Autansu Muhammad Abdullahi Umar wanda ya kammala Jami'ar ‘Regent’s University’ dake Landan inda ya yi digirinsa na farko a bangaren 'Global Management (Enterprise & Innovation)'.
![]() |
Muhammad Abdullahi Umar (daga dama sanya da rigar yayen dalibai) tare da iyayensa da sauran iyalai. |
An yi bikin ne a yau Talata 14 ga watan Satumban 2021. Abubakar
Aminu bai yi karin bayani kan bikin yayen daliban ba, sai dai hotuna da ya
wallafa har kashi biyu dangane da bikin yayen daliban.
Rahotanni
sun bayyana cewa; Babban dan Gwamnan jihar Kano, Abdul'aziz Ganduje ya maka
mahaifiyarsa Dr Hafsat Ganduje a gaban hukumar yaki da yi wa tattalin arziki
zagon kasa wato EFCC akan zargin da yake yi mata da almundahana da kuma azurta
kanta ta hanyoyin da yake ganin ba su dace ba.
Tuni
dai a bangaren Hukumar EFCC din ta aikewa da Dr Hafsat Ganduje mai dakin
Gwamnan Kano da goron gayyata domin ta je gaban Hukumar don amsa tambayoyi kan zargin
da dan na ta ke yi mata, amma ta ki amsa gayyatar ba tare da kuma ta bayar da
wani uzuri a rubuce ba.
A
cikin wasikar da Abdul'aziz Ganduje ya aikewa da EFCC, ta shafi badakalar
filaye da kuma miliyoyin kudade. Sai dai Kakakin Hukumar EFCC Wilson Uwujaren
bai ce uffan ba dangane da batun bayan an yi masa tambaya a kai.
Idan ba a manta ba, a baya an zargi Gwamnan Kano Alhaji Abdullahi
Umar Ganduje da yin badakala ta sama da dalar Amurka miliyan biyar, inda aka
nuno shi a wani faifan bidiyo yana sunkuma dalar Amurka daga cikin kudaden 'yan
kwangila, sai dai Gwamnan ya karyata bidiyon tare da kai karar jaridar Daily
Nigerian da mawallafinta Jaafar Jaafar gaban kotu game da batun bidiyon Dala.
![]() |
Muhammad Abdullahi Umar, Dan Autan Ganduje da ya kammala digirinsa na farko |
No comments