Daga Ammar Muhammad A wata takarda da Hukumar tsara birane da ci gaba ta jihar Kaduna wato KASUPDA ta rabawa mutanen Unguwar Hayin Dan...
Daga
Ammar Muhammad
A wata
takarda da Hukumar tsara birane da ci gaba ta jihar Kaduna wato KASUPDA ta
rabawa mutanen Unguwar Hayin Danmani dake jihar Kaduna, ta nemi da su kwashe
tarkacensu dake Unguwar nan da kwanaki 21 idan ba haka ba gwamnatin za ta zo ta
rusa gidajen dake Unguwar kuma su biya ladan rusawa.
Hukumar
ta yi wa mazauna Unguwar gargadin ne a cikin wata takarda da ta raba musu mai
dauke da kwanan watan 7 ga watan Satumban 2021.
Takardar
mai dauke da lamba PS/OFF/COM/2004 ta shaida mazauna Unguwar Hayin Danmani
Residential Layout (TPO689) cewa; gine-ginen an yi su ne ba bisa ka’ida ba
domin Hukumar tsara Birane ta jihar Kaduna ba ta sahhale a yi gine-gine a wurin
ba, wanda suka ce hakan ya sabawa dokar sashe na 27 sakin Layi na 1.
“Hukumomi
sun lura cewa kun keta wurin Gwamnatin jihar Kaduna (TPO 689) Hayin Danmani
Layout Kaduna ba bisa ka’ida ba, inda kuka yi gine-gine ba tare da samun takardar
izinin haka daga KASUPDA ba wanda hakan ya sabawa dokar sashe na 27 (1)”, inji
takardar kamar yadda MADOGARA ta samu kwafi.
Takardar
ta ci gaba da cewa; “bisa wadannan hujjoji, mun ba ku kwana 21 daga kwanan
watan da kuka sami kwafin takardar nan ta wa’adin tashi da ku cire dukkanin
abubuwanku masu amfani a wurin, idan ba ku yi haka ba, hukuma ba ta da wani
zabi da ya wuce mu rusa dukkanin gine-ginen da kayayyakin kuma ku biya ladan
rusawa kamar yadda doka ta sashe 60 da 62 ta tanada”, suka tabbatar.
Isma’il
Umar Dikko, Babban Daraktan Hukumar ta KASUPDA shi ne ya sanyawa takardar hannu
a madadin gwamnatin jihar Kaduna.
Manazarta
sun kiyasta cewa akalla akwai gidaje 660 a Danmani Kaduna, wanda idan gwamnati
ta rushe Unguwar, Rusau din zai shafi akalla mutane 10,000.
No comments