Ministan sadarwa a Nijeriya ya ce gwamnatin na kokarin lalubo hanyoyin amfani da fasahar zamani wurin shawo kan matsalar tsaro, da ya hada...
Ministan sadarwa a Nijeriya ya ce gwamnatin na kokarin lalubo hanyoyin amfani da fasahar zamani wurin shawo kan matsalar tsaro, da ya hada da amfani da mutum mutumin kwamfuta kamar yadda BBC ta labarto.
Isa Ali Pantami ya shaida hakan ne yayin jawabi a wani taro kan tsaro da Hukumar tsaron fararen hula ta Nijeriya, wato NSCDC ta shirya ranar Talata.
Ministan ya kuma shawarci hukumomin tsaron Najeriya da su rungumi damar da ta samu ta amfani da manhajar 5G wurin shawo kan matsalar tsaro.
An shirya taron ne da nufin samar da hadin kan hukumomin tsaron Najeriya wurin samar da tsaro.
No comments