Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Allah Wadai Da Juyin Mulkin Da Aka Yi A Ƙasar Guinea

 


Gwamntin Nijeriya ta ce ta ta damu matuƙa da juyin mulkin da ya faru a ƙasar Guinea a ranar Lahadi. 

Cikin wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen Nijeriya ta ce: "gwamnatin Nijeriya ta yi Allah wadai da juyin mulkin tare da bayyana cewa matakin ya saɓawa tsarin dimokuradiyya na ƙungiyar ECOWAS"

Sannan kuma sanarwar ta yi kira ga sojojin da suka yi juyin mulkin su gaggauta mutunta kundin tsarin mulki tare da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al'ummar kasar.


Post a Comment

0 Comments