Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Hutun Mako Biyu Ga Angwayen Karni

  Gwamnatin Tarayya ta amince da hutun mako biyu ga ma’aikata maza da matansu da suka haihu, wato angwayen karni, abin da ke nufin wani babb...

 


Gwamnatin Tarayya ta amince da hutun mako biyu ga ma’aikata maza da matansu da suka haihu, wato angwayen karni, abin da ke nufin wani babban sauyi a tsarin dokokin aiki na Nijeriya.

Matakin ya zo ne bayan da aka shafe shekaru biyu ana muhawara kan batun.

Shugabar Ofishin Ma’aikatan gwamnatin Nijeriya Folasade Yemi-Esan ta ce an amince da matakin ne bayan taron majalisar koli a yau Laraba, “don iyaye maza su samu sukunin kasancewa da jariransu a farko-farkon haihuwa.”

Ta ce mazan da matansu suka haihu da wadanda suka karbi rikon jaririn da bai wuce wata hudu ba ne za su mori wannan hutu.

Matakin gabatar da hutun haihuwa ga angwayen karni na zuwa ne a lokacin da masu fafutuka suke ci gaba da neman cewa ya kamata maza ma a dinga ba su hutun haihuwa don su samu lokacin kula da matansu da jariransu – a wani kokari na sauya al’adar da ake barin mata kawai da dawainiyar haihuwa.


No comments