Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Gwamnatin Zamfara Ta Rufe Dukkanin Makarantun Jihar

  Gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun faɗin jihar kamar yadda BBC Hausa ta labarto. Kwamishinan ƴan s...


 

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun faɗin jihar kamar yadda BBC Hausa ta labarto.

Kwamishinan ƴan sandan jihar CP Ayuba N Elkana wanda ya tabbatar da ɗaukar matakin ga manema labarai a ranar Laraba ya ce matakin ya shafi makarantun sakandare da na firamare

Sannan kuma ya sanar da sanya dokar hana fitar dare a dukkanin ƙananan hukumomin jihar 14.

Dokar za ta fara aiki daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a ƙananan hukumomi 13.

A garin Gusau babban birnin jihar, dokar za hana fita za ta fara aiki daga ƙarfe 8 na yamma zuwa ƙarfe 6 na safe.

Wannan na zuwa ne sa'o'i bayan samun labarin sace ɗaliba da dama a wata makarantar sakandare ta Kaya a yankin Maradun.

 

No comments