Gwamnatin Tarayya ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin babbar kotun jihar Oyo wacce ta ce a bayar da diyyar Naira Biliyan 20 kan Babban L...
Gwamnatin
Tarayya ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin babbar kotun jihar Oyo wacce ta
ce a bayar da diyyar Naira Biliyan 20 kan Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF)
da Hukumar Tsaro ta DSS saboda zargin mamaye gidan Sunday Adeyemo da Hukumar
DSS ta yi a ranar 1 ga watan Yuli.
Kotun
da ke zama a Ibadan ta bayar da wannan umurnin bayar da wannan diyyar ne a
cikin karar kare hakkin dan adam wanda mai fafutukar kafa kasar Yarbawa,
Adeyemo, wanda aka fi sani da Igboho, ya kai a kan wadanda yake tuhumar saboda
mamaye gidansa da ke yankin Soka a babban birnin jihar Oyo.
AGF,
Mista Abubakar Malami (SAN), duk da haka, ya shaida cewa a ranar Juma’a
Gwamnatin Tarayya za ta daukaka kara kan hukuncin, kuma tuni aka fara shirin
daukaka karar.
Lauyan
Igboho, Mista Yomi Aliyu (SAN), shi ne wanda ya shigar da kara na neman hakkin
bil adama da yake ganin an take wa wanda yake bai wa kariya, inda ya nemi AGF,
DSS da Daraktan DSS na Oyo su biya Naira Biliyan 500.
No comments