Hukumomin Gambia Na Nuna Damuwa Kan Ƙulla Kawancen Siyasa Da Yahya JammehShugaban hukumar sassanci a Gambia ya nuna rashin dadinsa kan kawance tsakanin jam’yyar shugaba Adama Barrow da tsohon shugaban da ya mulki kasar na tsawon lokaci Yahya Jammeh.

Sun hada-kai gabannin zabukan da ke tafe a watan Disamba.

An kafa hukumar sassanci ta TRRC a shekara ta 2017, bayan Jammeh ya tsere daga kasar sakamakon shan kaye da korafe-korafen cin zarafi da suka biyo baya.

Masu korafin na cewa tsohon shugaban ya aikata kisa da azabtar wa kan abokan adawa da cin zarafi ta hanyar lalata a mulkinsa na sama da shekaru 20.

Hukumar TRRC na shirin gabatar da rahotonta da ta tattara ga shugaba Barrow na gaba kadan, amma shugabanta, Baba Galleh Jallow ya shaida wa BBC cewa akwai abubuwa da dama da ba lallai a amince da su ba saboda sabuwar kawancen.


-BBC Hausa

Post a Comment

0 Comments