Daga Muhammad A. Dalhatu Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da Dattawan kabilar Ibo dake Kudu maso gabashin Nijeriya a ga...
Daga Muhammad A. Dalhatu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da Dattawan kabilar Ibo dake Kudu maso gabashin Nijeriya a garin Owerri ta jihar Imo.
Majiyarmu ta Jaridar Daily Trust ta labarto cewa; an hana manema labarai shiga wurin taron. Taron dai ya gudana ne a katafaren sabon ginin zamani da aka kaddamar a gidan gwamnatin Imo dake Owerri.
Wadanda suka kasance a taron sun hada da gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, da mataimakin Gwamnan jihar Abia Ude Okechukwu.
Sauran sun hada da shugaban kungiyar Ibo ta duniya ta Ohanaeze Ndigbo Worldwide, Farfesa George Obiozor; Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyema; Ministan jiha, Cif Uche Ogar: da sauran jiga-jigan jam’iyyar.
Tuni shugaba Buhari ya kaddamar da aikin titin Ihiagwa zuwa Nekede, da kuma gadar karkashin kasa ta zamani ta ‘Balloon’, da kuma hanyar ruwa a titin Chukwuma Nwoha, da titin Naze/ Nekede/Ihiagwa, da sauran su.
Wasu manazarta na ganin ganawar na da alaka da tashin-tashina na matsalar tsaro dake faruwa a yankin da kuma batun kama shugaban 'yan Awaren kafa kasar Biyafara, Nnamdi Kanu da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi.
No comments