Hukumar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), ta taya Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin zaman...
Hukumar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta
Nijeriya (MAAUN), ta taya Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani, Dakta
Isa Ali Ibrahim Pantami murnar samun matsayin Farfesa a bangaren tsaron yanar
gizo.
Pantami yana cikin masu bincike guda bakwai (Mataimakin Farfesoshi) da Hukumar gudanarwa ta Jami'ar Fasaha ta Tarayya
dake Owerri (FUTO)
ta ɗaukaka zuwa Farfesa a zamanta na 186 da aka yi ranar Juma'a 20 ga watan Agustan 2021.
Sakon taya murnar na dauke ne a cikin wata sanarwa da shugaba kuma
wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American
University da kuma Franco-British International University dake Kaduna, Farfesa
Adamu Abubakar Gwarzo wanda aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Litinin.
Ya ce, daukaka darajar Dakta Pantami da Jami’ar FUTO ta yi zuwa
matsayin Farfesa an yi shi a lokacin da ya dace duba da cewa shi masanin
bincike ne na duniya, mai ilimi ne, mai tsara manufofi ne, kwararre kan sha’anin
doka kuma Malami da ke da wallafe-wallafe sama da 160 da sunansa.
"Pantami ya sami lambobin yabo sama da 130 a ciki da wajen Nijeriya,
kazalika ya samu lambobin yabo a matsayin ministan da ya fi kowa a Nijeriya",
in ji Farfesa Abubakar Gwarzo.
Shugaban Jami’ar ta MAAUN ya bayyana Farfesa Pantami a matsayin
jajirtaccen matashi kuma masani wanda ya ba da gudummawa ga ci gaban Nijeriya a
lokacin da ya rike shugabancin NITDA da kuma matsayin da yake na matsayin
Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani.
Farfesa Abubakar Gwarzo, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar
Jami’o’i Masu zaman kansu na Afirka ya ce, “A madadin hukumar gudanarwa na
MAAUN, ina taya Minista murnar daukaka darajarsa zuwa Farfesa”.
"Ina taya Malamai masani kuma mai ba ni shawara- dan Afirka na farko da aka taba nada wa a matsayin shugaban sashe (H.O.D) kuma Shugaban sashen Rubutun Fasaha a Jami'ar Musulunci ta Madinah a 2014," in ji Farfesa Abubakar Gwarzo.
Ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya bai wa Farfesa Pantami hikima,
kwarin gwiwa domin ya ci gaba da ba da na shi gudummawar wajen ci gaban kasarnan.
No comments