Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Maryam Abacha American University dake Nijer, ta mika sakon ta’aziyyarta ga Iyaye da ‘yan’uwan daya daga ciki...
Hukumar
gudanarwa ta Jami’ar Maryam Abacha American University dake Nijer, ta mika sakon
ta’aziyyarta ga Iyaye da ‘yan’uwan daya daga cikin dalibanta, Muhammad Ahmad
Aisami, wanda ya rasu sakamakon hadarin mota a titin Gubio zuwa Maiduguri a
ranar Litinin din 13 ga watan Agustan 2021.
Marigayi
Muhammad Aisami yana matakin aji biyu ne (200 level) A Jami’ar a sashen gudanar
da al’umma (Public Administration).
Sakon
ta’aziyyar na dauke ne da sa hannun shugaba kuma mu’assasin Jami’ar Maryam
Abacha American University da Franco-British International University dake
Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, wanda aka raba wa manema labarai kwafinta
a Kano a ranar Talata.
Hukumar
gudanarwa ta Jami’ar ta bayyana rasuwar dalibin a matsayin babban rashi ba
kawai ga Iyayensa da ‘yan’uwansa ba, ga dukkanin ma’aikatan makarantar.
Shugaban
MAAUN har wala yau ya bayyana Marigayin a matsayin dalibi mai ladabi wanda ke
girmama Dattawa, musamman Malamansa.
Farfesa
Abubakar Gwarzo ya ce "A madadin Hukumar Gudanarwar ta Jami'ar Maryam
Abacha American University ta Nijer, ina mika sakon ta'aziyya ga iyaye, 'yan
uwa da abokan Muhammad Ahmad Aisami bisa rasuwarsa." Inji Farfesa Abubakar Gwarzo.
Ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya sanya Marigayin a Aljannah
Firdaus ya kuma bai wa iyalansa jure wannan rashin da ba za a iya maida shi ba.
No comments