Wani jirgin yaki ba a tantance daga ina yake ba ya yi aman wuta a yankin kauyen Buhari da ke karamar Yunusari a jihar Yobe da safiyar La...
Wani
jirgin yaki ba a tantance daga ina yake ba ya yi aman wuta a yankin kauyen
Buhari da ke karamar Yunusari a jihar Yobe da safiyar Laraba, inda ya yi
sanadin mutuwar fararen hula da dama.
Al'ummar
garin sun ce shaida wa BBC cewa sun wayi gari ne da ganin jiragen yaki har uku
suna shawagi a sararin samaniyar garin nasu.
Daga
bisani daya daga cikin jiragen ya yi aman wuta kan wani bangaren garin, kamar
yadda wani da 'yan uwansa suka mutu a lamarin ya shaida wa BBC.
BBC
ta tuntubi runudnar 'yan sandan jihar Yobe inda Kakakinta ASP Dungus
Abdurrahman ya ce ba su samu labarin ba, amma za su tuntubi BBC idan suka samu
labarin.
"Da
safe kamar karfe 8.30 ne abin ya faru, har zuwa lokacin da daya daga cikin
jiragen ya fado wani bangaren na garin yana ta zubar da wuta, duk gidajen da ke
wannan bangaren sai da suka lalace.
"Jirgin
babba ne sosai irin na sojoji, amma ba mu san na ina ne ba," in ji shi.
Ganau
din ya ce ba za su iya sanin adadin mutanen da suka rasu ba zuwa yanzu,
"don ko a cikin gidanmu ma mun rasa mutum biyu," in ji shi.
Ya
ce cikin mamatan gidansu akwai matar babansa da 'yar yayarsa, "amma ni ba
na gida lokacin muna gefen gari a kan idonmu komai ya faru.
Sai
dai ya ce har yanzu babu jami'in tsaron da ya je wajen, "don da akwai
yaran Boko Haram da ke shawagi sosai a yankin."
Ganau
din ya ce su 'yan gari ya su-ya su ne suka yi aikin kwasar gawarwaki da wadanda
suka jikkata zuwa asibitin garin Geidam, saboda rashin kyawun sadarwa ma ba zai
sa su tsaya bata lokacin yin waya ba, kamar yadda ya ce.
Shi
ma wani mazaunin garin da aka je asibitin Geidam da shi ya cewa BBC halin da
wadanda suka jikkatan ke ciki ba shi da dadin gani sam.
"Idan
ka kalle su ba za ka iya sake kallonsu ba don duk suna cikin jini kaca-kaca
babu dadin gani.
"Da
idona na ga mutum 19 da suka jikkata. Akwai wadanda suka rasu da dama kuma amma
ba a san adadinsu ba don an bar su a can garin Buharin.
"Ni
ma akwai dangina hudu da suka jikkata," ya ce.
Amma
mutumin ya ce a can Geidam akwai jami'an tsaro da dama da suka zagaye asibitin.
No comments