Kamfanin MTN Ya Sabunta Lasisinsa A Nijeriya Zuwa Shekaru 10 Masu Zuwa


Kamfanin sadarwa na MTN ya sabunta lasisinsa a Nijeriya har zuwa wasu shekaru 10 daga watan Satumbar nan. 

MTN ya ce ya biya naira biliyan 71.6 domin sabunta lasisinsa a Nijeriya, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito.

Lasisin kamfanin ya Ζ™are ne a ranar 31 ga Agustan 2021, kuma yanzu ya sake sabunta lasisin wanda ya fara aiki a ranar 1 ga Satumba.

Post a Comment

0 Comments