Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Kotu Ta Umurci Gwamnatin Nijeriya Ta Biya Igboho Diyyar Naira Biliyan 20

  Wata babbar kotu a jihar Oyo da ke a birnin Badun, arewa maso yammacin Najeriya ta umarci gwamnatin Najeriya ta biya diyyar naira biliyan ...

 


Wata babbar kotu a jihar Oyo da ke a birnin Badun, arewa maso yammacin Najeriya ta umarci gwamnatin Najeriya ta biya diyyar naira biliyan 20 ga matashin nan Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Igboho, a matsayin diyyar barnar da jami'an tsaron farin kaya na DSS suka yi masa yayin wani sumame da suka kai gidansa.

Dan rajin awaren na yankin kudu maso yamamcin Najeriya na hannun hukumomin Benin a halin da ake ciki tun bayan tserewarsa lokacin da jami'an na DSS din suka dira a gidansa da tsakar dare.

DSS dai ta bayan kwashe tsawon lokaci tana musayar wuta da wasu mutane da ta tarar a gidan lokacin da jami'anta suka isa, ta samu nasarar kama tarin manyan makamai a gidan, wadanda aka mallaka ba bisa ka'ida ba.

Bayan tserewar Igboho din ne sai lauyoyinsa suka maka hukumar ta DSS da ministan shari'a na Najeriya a gaban kuliya, inda a madadinsa, suke neman a biya shi makudan kudade saboda take hakkinsa na dan kasa.

Jaridar Punch Nigeria ta ce a hukuncin da aka yanke a yau Juma'a alkalin kotun ya umarci a biya Igboho Naira Biliyan 20 a matsayin diyya, kasa da abun da lauyoyinsa suke nema tun da farko.


-BBC

No comments